Labaran Yau Laraba 02/08/2023CE - 15/01/1445AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.
Gwamnatin Bola Tinubu za ta batar da N100bn domin a shuka rogo, alkalama, shinkafa da masara.
Majalisar wakilai za ta binciki sayar da helikwaftan da gwamnatin Buhari ta yi.
Shugaba Bola Tinubu ya bar birnin Abuja zuwa Cotonou don halartar bikin cika shekara 63 da kafa Jamhuriyar Benin.
Wani jirgin sama mai saukar angulu da ba a kai ga tantancewa ba ya yi hatsari a kan wani gini da ke unguwar Ikeja a Jihar Legas.
Yan sanda sun cafke wani dan kasuwa dan kasar Kamaru bisa zargin damfarar N26.7ma Legas.
Sojoji sun tarwatsa wasu sansanonin IPOB/ESN a Anambra da Imo.
Hukumar Kula da Asibitocin Kano, ta sallami manyan jami'an lafiya na asibitoci 3 da ke jihar.
Gwamna Fintiri ya amince zai yi katangar tsaro ga sansanin masu yi wa kasa hidima (NYSC) a Girei dake Adamawa.
Rundunar 'Yan Sandan Kano za ta fafata wasan sada zumunta tsakaninta da 'Yan Kannywood da Tiktok.
Gwamnan jihar Kwara ya umarci a raba wa dalibai haifaffun jiharsa tallafin N10,000 domin rage raÉ—adin cire tallafi.
Ma'aikatan Hukumar Kula da Man Fetur na zanga zanga kan makalewar albashinsu na wata 7, da sauran hakkokinsu a shalkwatar hukumar da ke Abuja.
Juyin mulki: Sojojin Nijar sun kama mutane 180 daga tsohuwar gwamnati.
Faransa da Italiya za su fara kwashe ‘yan kasarsu daga Nijar.
An yi harbe-harbe cikin dare a birnin Ouagadougou na Burkina Faso.
Jamus ta bukaci ‘yan kasar ta dake Nijar da su shiga jirgin Faransa domin barin kasar.
’Yan Sanda Sun Kama Mutumin Da Ake Zargi Da Lalata Yara 91 a Australia.
An nada Van Dijk a matsayin Kyaftin din Liverpool.