Labaran Yau Alhamis Nigeria da Niger 10/08/2023CE - 23/01/1445AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.
Tsohon Sarkin Kano Khalifa Sanusi ya gana da shugaban Nijar Janar Tchiani a Yamai.
Zargin daukar ma'aikata ba bisa ka'ida ba Hukumomi Cibiyoyi da Ma’aikatu 35 sun Æ™i bayyana a gaban kwamitin bincike.
Muhammad Sanusi II ya gana da Shugaba Tinubu bayan dawowa daga Jamhuriyyar Nijar, sannan yace “Za mu cigaba da yin bakin kokarinmu na jawo bangarorin 2 domin a kara samun fahimta."
Sojoji sun kashe Æ´an bindiga 3 sun kama makamai da dama a karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna.
Ba ma goyon bayan amfani da ƙarfi kan Nijar, malaman Najeriya suka faɗa wa Tinubu.
Badakalar Kudade: Kotu ta tsayr da 30 ga Agusta don yanke hukunci kan zargin da ake yi wa tsohon Gwamnan Zamfara Matawalle.
Matashi ya kashe tsoho da tabarya saboda zargin maita a jihar Gombe.
Sanatocin Kudu maso gabas a majalisar dattawan Najeriya, sun bukaci karin kujerun Ministoci daga wajen Bola Ahmed Tinubu.
Dakarun Tarayya sun kori mayaƙan sa-kai daga Amhara a kasar Habasha.
Mohamed Bazoum ya yi korafin cewa sojojin suna tilasta masa cin busasshiyar shinkafa da taliya.
Wutar daji da guguwa sun tilasta kwashe mutane a jihar Hawaii a Amurka.
Faransa ta musanta zargin kai hari a Nijar.
An harbe dan takarar shugaban kasa a Ecuador.
Chelsea ta yanke shawarar watsi da tattaunawar musayar Dusan Vlahovic, da Romelu Lukaku.
Chelsea na gab da kammala yarjejeniyar Moises Caicedo Brighton, sun kuma kagu su kallama komai domin ya fara wasan farko a asabar din nan a karawar da za su yi da Liverpool.
Join our Whatsapp group👇👇