Labaran Yau Alhamis 29/06/2023CE - 11/12/1444AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.

0

Labaran  Yau Alhamis 29/06/2023CE - 11/12/1444AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.






Shugaban Kasa Tinubu ya gudanar da Sallar Idinsa a filin Idi da ke barikin sojoji na Dodanbda ke Jihar Legas a ranar Laraba.


Tinubu ya buÆ™aci Æ´an Najeriya su mayar da al'amuransu ga Allah. 


Manyan hafsoshin Najeriya sun yaba wa dakarun Æ™asar da ke fagen daga. 


Gwamnan Kano ya sa al’umma da-dama cikin farin ciki, ‘yan fansho sun samu hakkokinsu, ma'aikatan da su ka yi ritaya sun yaba.


Mataimakin gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam, ya tabbatar wa al'umma cewa gwamnati ta kowa ce, ba tare da la’akari da banbancin siyasa ba.


Bikin Babbar Sallah: Gwamnan Katsina yayifatali da kyautar raguna 100 da wani attajiri yayi masa


Boko Haram ta kashe wani shugabanta kan yunkurin yin tawaye. 


Sakataren gwamnatin Zamfara ya sha alwashin yin abin da ya kira gyara kura-kuren da Bello Matawalle ya yi a mulki. 


Gwamna Adeleke Ya Gaza Yin Sallar Idi Sakamakon Wani Sanata Da Ya Tsare Masa Wuri. 


Kotu tarayya mai zamanta a Abuja, ta dakatar da gwamnatin jihar Kano, daga sake cafke Alhassan Doguwa kan zargin kisan kai. 


Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi sallar Idi a Masallacin Idi da ke Miller Road a unguwar Bompai a Jihar Kano.


Yunwa ta kashe mutane a Habasha saboda rashin tallafi. 


ÆŠan sanda ya harbe wani matashi a Faransa. 


Rikicin Sudan na neman rikidewa zuwa na kabilanci. 


'Yan ta'adda sun kashe sojin Burkina Faso da 'yan sa kai sama da 30.


Majalisar dokokin Chadi ta amince da daftarin sabon kundin tsarin mulki. 


Harry Kane ya nuna sha'awar komawa Bayern Munich.

Post a Comment

0 Comments
Post a Comment (0)
To Top